Tsohon Shugaban APC na Kebbi, Muhammadu Besse, Ya Rasu a Hannun ’Yan Bindiga

Tsohon shugaban jam’iyyar APC a Jihar Kebbi, Alhaji Muhammadu Besse, ya rasu a hannun ’yan bindiga bayan da aka sace shi tun a farkon watan Yunin 2026.

Labarin rasuwarsa ya fito ne ta cikin wani rubutu da ɗan jarida mai bibiyar harkokin tsaro da ta’addanci, Bakatsine, ya wallafa a shafinsa na X. Bakatsine ya shahara wajen bayar da rahotanni kan ayyukan ’yan ta’adda da matsalolin tsaro musamman a yankin Arewa maso Yammacin Najeriya.

Kafin wannan lokaci, ’yan bindigar sun fitar da wani bidiyo da ya nuna Alhaji Besse tare da wani mutum, inda aka ga ana cin zarafinsu yayin da suke hannunsu.

Rahotannin da suka fito na baya-bayan nan sun nuna cewa mutanen biyu da aka gani a cikin bidiyon sun rasa rayukansu a hannun ’yan bindigar.

Rasuwar Alhaji Muhammadu Besse ta ƙara jawo damuwa kan matsalar rashin tsaro da ci gaba da sace mutane domin neman kuɗin fansa a yankunan Arewa maso Yammacin Najeriya.

Comments (0)
Add Comment