Wani tsagin PDP a jihar Jigawa ya ayyana Yakubu Mu’azu Gwaram a matsayin ɗan takarar gwamnan jihar Jigawa na 2027

Wani tsagi a jam’iyyar PDP ta sanar da cewa Hon. Yakubu Mu’azu Gwaram ne ya zama ɗan takarar gwamnan Jihar Jigawa na jam’iyyar a zaɓen shekarar 2027.

Sanarwar ta fito ne bayan kammala zaɓen fidda gwani na jam’iyyar da aka gudanar a faɗin jihar.

Da yake bayyana sakamakon zaɓen, jami’in tattarawa da sanar da sakamakon zaɓen PDP a Jihar Jigawa, Yakubu Magaji, ya ce Yakubu Mu’azu Gwaram ya cika dukkan sharuddan da kundin tsarin jam’iyyar ya tanada domin zama ɗan takarar gwamna.

Ya bayyana cewa Gwaram ya samu kuri’u 1,436 daga wakilan mazabu 237 da ke faɗin Jihar Jigawa, lamarin da ya tabbatar da nasararsa a zaɓen fidda gwanin.

Sakamakon hakan, jam’iyyar PDP ta ayyana Yakubu Mu’azu Gwaram a matsayin wanda zai riƙe tutar jam’iyyar a zaɓen gwamnan Jihar Jigawa da za a gudanar a shekarar 2027.

Sai dai wannan sanarwa na zuwa ne mako guda bayan wani tsagin PDP ya ayyana Mustapha Sule Lamido a matsayin ɗan takarar gwamnan jam’iyyar.

Lamarin ya nuna yadda rikicin cikin gida ke ci gaba da addabar jam’iyyar a Jigawa, inda tsagin daban-daban ke gudanar da matakan siyasa masu cin karo da juna dangane da zaɓukan fidda gwani.

Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, babu wata sanarwa ta haɗin gwiwa daga shugabancin jam’iyyar ta ƙasa da ta warware saɓanin da ke tattare da ayyana ’yan takarar biyu.

Comments (0)
Add Comment