Wasu ‘yan majalisa da aka dakatar a jihar Zamfara sun nada sabon kakakin majalisa

Rikici ya barke a Majalisar dokokin Jihar Zamfara, yayin da wasu ‘yan majalisa goma da aka dakatar suka kafa nasu bangare tare da zaben Hon. Bashar Aliyu Gummi a matsayin sabon kakakin majalisa.

Wannan bangaren ya kunshi ‘yan jam’iyyar APC da PDP, inda suka ba Gwamna Dauda Lawal wa’adin wata guda ya magance matsalolin tsaro ko kuma a tsige shi, tare da bukatar ya mika kasafin kudin bana cikin lokaci.

A martanin da ya biyo baya, kakakin majalisar Bilyaminu Moriki ya bayyana taron da aka yi a wani wuri daban da zauren majalisa a matsayin ba bisa ka’ida ba, yana mai cewa hukuncin kotu ya umurci a ci gaba da bin tsarin da ake kai.

A halin yanzu, majalisar ta dakatar da ‘yan majalisa goma, inda suka zargi su da kutsa ofishin sakataren majalisar da neman sandar shugabanci ba bisa ka’ida ba, yayin da wadanda aka dakatar din suka ce ana barazana da rayukansu, kuma sun shigar da kara a kotu domin neman ‘yancinsu.

Comments (0)
Add Comment