Wata kungiya ta raba kayan abinci ga fursunoni a jihar Nasarawa

Kungiyar mai zaman kanta da ake kira Islamic Society of Eggonland (ISE) ta ba da abinci da darajarsa ya kai miliyoyin Naira ga fursunonin da ke karamar hukumar Wamba a jihar Nasarawa.

Babban sakataren kungiyar ta kasar Ingila, Umar Abdullahi Galle sa’ad da yake ba da kayan, ya ce abincin ya ƙunshi: buhu biyar na shinkafa, buhu biyu na alkama, buhu biyu na alkama, buhun sukari biyu, buhun gishiri guda 1, sauran sun hada da kwali biyu na kifi, kwali 2 na Maggie cube da kuma jarkar mai.

Comments (0)
Add Comment