Wike Ya Kai Ƙungiyar Ma’aikatan FCTA Ƙara Kotu Kan Yajin Aiki

Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike, ya kai ƙungiyoyin ma’aikatan FCTA ƙara kotu kan yajin aikin da suke yi a Abuja.

Ma’aikatan FCTA da FCDA sun tsunduma yajin aiki na dindindin bayan wa’adin kwana bakwai da suka bayar ya ƙare ba tare da biyan buƙatunsu ba.

Yajin aikin ya rufe manyan ofisoshin gwamnati a Abuja, lamarin da ya sa jami’an tsaro suka kulle sakatariyar FCTA.

Duk da ikirarin gwamnatin FCTA cewa ta biya mafi yawan buƙatun ma’aikata. ƙungiyar JUAC ta musanta hakan tana mai cewa har yanzu ba a warware matsalolin ba.

An shigar da ƙarar ne a Kotun Kwadago ta Ƙasa da ke Abuja, inda ministan da FCTA ke neman kotu ta hana ƙungiyoyin ma’aikata ci gaba da toshe ofisoshi da hanyoyi.

Alkalin kotun, Mai shari’a E.D. Subilim, ya amince a yi wa shugabannin ƙungiyar hidimar sammaci ta hanyar wallafa shi a jarida da mannawa a ofishinsu.

Sai dai ƙungiyar JUAC ta ce ba za ta dakatar da yajin aikin ba, tana mai jaddada cewa za su ci gaba da zama a gida har sai an biya buƙatunsu.

Comments (0)
Add Comment