‘Yan jam’iyyar PDP tsagin Nyesom Wike, za su yi taro yau a Abuja domin tattauna kan kafa kwamatin riko da kuma shirin gudanar da sabon taron jam’iyyar na kasa (National Convention), yayin da wa’adin shugabancin jam’iyyar zai ƙarewa a 9 ga Disamba, 2025.
Tsagin Tanimu Turaki kuwa sun ce su ke rike da iko da shugabancin jam’iyya na gaskiya, suna kuma kiran duk wani taro na tsagin Wike zai gudanar a matsayin sabawa doka.
Tun bayan rufe hedkwatar jam’iyyar dake Wadata Plaza a ranar 19 ga Nuwamba, 2025; NWC na bangaren Turaki na gudanar da ayyukan jam’iyya daga wani ofis na wucin gadi a Area 10, Abuja.
Rikicin shugabanci a PDP na kara tsananta, yayin da bangarorin biyu ke ƙoƙarin tabbatar da ikonsu bisa shugabancin jam’iyyar kafin zaben 2027.