Yadda aka kashe kwamishina a jihar Katsina ta hanyar daɓa masa wuka

An rawaito cewa wadanda suka kashe shi sun kashe shi ne a gidansa dake rukunin gidaje na Fatima Shema a birnin Katsina, inda suka ja gawarsa suka bandaki suka kulle ta.

Wata majiya tace a jiya aka kashe shi, yayin da wata majiyar tace a yau aka kashe shi. An kuma tattaro cewa shi kadai ne a gidan lokacin da aka kashe shi. Majiyar tace yaron gidansa ne ya fara jawo hankalin jama’a dangane da kisan bayan yazo gidan ya tarar da jini a kasa yau da rana.

Mamacin a baya shine mai bawa Gwamna Aminu Bello Masari shawara akan kimiyya da fasaha, kafin daga bisani a kara masa girma zuwa kwamishina.

A halin da ake ciki, kwamishinan yansanda na jihar Katsina, Sanusi Buba, yace tuni aka kama wani da ake zargi da hannu a kisan kwamishinan.

Comments (0)
Add Comment