Rundunar Yansanda jihar Katsina da ke arewa maso yammacin Najeriya, ta yi karin haske kan wani mummunan hatsarin mota da ya yi sanadin mutuwar mata 16 ‘yan kai amarya bayan motar da suke ciki ta yi taho mu gama da wata motar.
Yansandan sun ce suna tunanin hatsarin ya rutsa da amaryar amma ba su tabbatar da ko har da angon ba a hatsarin da ya afku a tsakanin Dutsimma zuwa Karofi.
Motoci ne dai suka yi karo da juna inda kuma suke dauke da mutum 30 a cikin su.
Shamsudeen Babajo, kakakin hukumar kula da kiyaye hadura ta jahar Katsina, ya shaida wa BBC cewa, hadarin ya afku ne a ranar Asabar, 31 ga watan Janairun 2026.
Ya ce, bincike ya nuna cewa motar da ta dauki ‘yan kai amaryar na kan gudu ne a lokacin da lamarin ya afku.
Ya ce.” A cikin motocin da suka yi taho mu gama da juna akwai mutum 30, kuma 16 daga cikinsu duk mata sun rasu, sai kuma mutum hudu wadanda ba su ji ciwo ba, 10 kuma sun samu rauni inda tuni aka kai su asibiti.”