’Yan Bindiga Sun Bukaci Al’ummar Kebbi Su Biya Naira Miliyan 100 Ko Su Kai Musu Hari

Wasu ’yan bindiga da ke addabar sassan Kudancin Jihar Kebbi sun buƙaci al’ummar Utouno da ke ƙaramar hukumar Ngaski su biya Naira miliyan 100, tare da yin barazanar kai musu hari idan ba su biya musu buƙatar su ba.

Rahotanni sun ce an isar da wannan saƙo ne ta wata wasiƙa da aka aike wa shugabannin al’ummar yankin.

Barazanar na zuwa ne a daidai lokacin da ake fama da ƙara taɓarɓarewar tsaro a wasu sassan Kebbi da jihohin maƙwabta, inda ƙungiyoyin masu ɗauke da makamai ke kai hare-hare, sace mutane da kuma karɓar haraji ba bisa ƙa’ida ba a yankunan karkara.

A cikin wasiƙar, waɗanda suka aike da ita sun gargadi mazauna yankin da kada su ɗauki batun da wasa.

“Wannan ba wasa ba ne. Dole ku biya Naira miliyan 100. Idan kuka ƙi, za ku fuskanci sakamakon, kuma kada ku zargi kowa sai kanku. Ko da kun kira sojoji, ba za su iya hana mu ba,” in ji wasiƙar.

Sun kuma ambaci wani hari da aka kai wa al’ummar Woro da ke ƙaramar hukumar Kaiama a Jihar Kwara, inda aka ce an kashe mutane bayan an yi irin wannan gargaɗi amma ba a biya kuɗin ba.

Wasu mazauna yankin sun tabbatar da samun wasiƙar, suna masu cewa hakan ya jefa su cikin fargaba.

Wani mazaunin yankin, Abbas Alkali, ya ce an kai ƙorafin ga shugaban ƙaramar hukuma, kuma ya samu labarin cewa gwamnati da hukumomin tsaro na ɗaukar matakai.

Ya ƙara da cewa wasu mazauna sun fara barin yankin domin tsira, yayin da waɗanda ba su da inda za su je suka ce za su ci gaba da zama tare da addu’a.

Malam Sa’ad Suleiman, wanda tela ne, ya ce wasiƙar ta tayar da hankulan jama’a musamman a wannan lokaci na azumin Ramadan, yana mai kira ga gwamnati da ta samar da isasshen tsaro.

Shi ma wani jagoran al’umma, Malam Ibrahim Bello, ya ce ba su ɗauki barazanar da wasa ba, kuma suna roƙon a tura sojoji cikin gaggawa domin kare su.

Mai magana da yawun gwamnan Jihar Kebbi ya ce gwamnatin jihar ta fara ɗaukar matakan kariya, tare da tura jami’an tsaro zuwa yankin, ciki har da sintirin jiragen sama.

A wani labarin kuma, Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kebbi ta ce jami’anta sun fatattaki wasu da ake zargin mambobin ƙungiyar Lakurawa ne a kan hanyar iyakar Maje.

Kakakin rundunar ya ce maharan sun yi amfani da shanu a cikin dare domin ɓoye motsinsu, amma jami’an sashen yaƙi da ta’addanci sun tunkare su tare da tilasta musu ja da baya.

Comments (0)
Add Comment