Wasu ’yan bindiga sun kai hari garin Yankamaye da ke Karamar Hukumar Tsanyawa a Jihar Kano, inda suka haddasa firgici tare da kashe mutane uku.
Dan Majalisar Tarayya mai wakiltar Ghari da Tsanyawa, Engr. Sani Bala, ya tabbatar da gano gawarwakin mutane uku bayan harin.
Mazauna yankin sun ce maharan sun shiga garin ne suna harbe-harbe ba kakkautawa, lamarin da ya sa mutane da dama suka tsere domin neman tsira.
Rahotanni sun kuma bayyana cewa wasu mutane sun jikkata a harin, inda aka garzaya da su asibiti domin kula da lafiyarsu.
Al’ummar yankin sun yi kira ga jami’an tsaro da su kara daukar matakan kare rayuka da dukiyoyi tare da dawo da zaman lafiya a yankin.