Rundunar ’Yan Sanda ta Jihar Katsina ta tabbatar da kisan jami’an ’yan sanda uku a wani kwanton ɓauna da ake zargin ’yan bindiga ne suka kai a Ƙaramar Hukumar Bakori ta jihar.
Kakakin rundunar, Aliyu Abubakar, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Laraba a Katsina.
A cewarsa, lamarin ya faru ne a ranar Talata da misalin ƙarfe 12:44 na rana, lokacin da wasu jami’an ’yan sanda ke gudanar da sintirin yaƙi da laifuka na yau da kullum a hanyar Guga–Bakori, sai wasu ’yan bindiga suka kai musu hari.
Ya ce jami’an sun faɗa tarkon maharan ne, inda suka buɗe musu wuta, amma ’yan sandan sun mayar da martani tare da fatattakar maharan.
Aliyu Abubakar ya bayyana cewa jami’ai uku sun mutu sakamakon harbin da aka yi musu yayin musayar wuta, yayin da wasu jami’ai biyu suka jikkata.
Ya ƙara da cewa an garzaya da waɗanda suka jikkata zuwa wani asibiti da ke kusa, inda ake ci gaba da ba su kulawar lafiya.
Kakakin rundunar ya ce an fara bincike domin gano tare da cafke waɗanda suka aikata wannan harin.