’Yan Bindiga Sun Kashe Makiyaya Uku A Barikin Ladi da Ke Jihar Filato

An kashe makiyaya uku a daren Alhamis a kan hanyar Dorowa zuwa Jong da ke karamar hukumar Barkin Ladi a jihar Filato, a wani hari da shugabannin al’umma suka bayyana a matsayin kwanton bauna.

Shugaban Kungiyar Miyetti Allah Cattle Breeders Association of Nigeria reshen jihar Filato, Ibrahim Babayo, ya tabbatar da faruwar lamarin ga manema labarai a Jos ranar Juma’a.

Ya ce makiyayan na kan hanyarsu ta komawa garin Jong ne bayan sun halarci tafsirin Alkur’ani a makwabciyar Dorowa, lokacin da aka kai musu hari da misalin karfe 7:30 na dare.

Ya ce, “Suna kan hanyarsu ta komawa gida ne lokacin da wasu masu dauke da makamai suka yi musu kwanton bauna. Bayan sun harbe su, maharan sun kuma yi amfani da makamai masu kaifi wajen sare kan daya daga cikin wadanda aka kashe. Wannan danyen aiki ne da ya kamata kowa ya yi Allah-wadai da shi.”

Ya yi zargin cewa wasu matasan Berom ne suka aikata harin. Ya kuma bukaci hukumomi su gudanar da cikakken bincike tare da tabbatar da an gurfanar da wadanda ke da hannu a lamarin.

Babayo ya ce kungiyar ta bukaci mambobinta su kwantar da hankalinsu tare da kauce wa daukar fansa. Ya kara da cewa suna bukatar kariya daga gwamnati tare da tabbatar da adalci.

A nasa bangaren, shugaban kungiyar matasan Berom ta kasa, Solomon Mwantiri, ya musanta zargin cewa matasan Berom ne suka kai harin.

Ya ce jami’an tsaro, ciki har da sojoji da jami’an ‘yan sanda na yankin Barkin Ladi, sun ziyarci wurin da harin ya faru. Ya kuma bukaci hukumomin tsaro da su gudanar da bincike mai zurfi da adalci ba tare da nuna bangaranci ba.

Mai magana da yawun rundunar Operation Enduring Peace, Kyaftin Chinonso Oteh, ya tabbatar da faruwar lamarin.

Ya ce rundunar ta samu labarin harin da misalin karfe 11 na dare a ranar Alhamis, inda nan take aka tura sojoji zuwa yankin.

Ya kara da cewa babban kwamandan rundunar ta 3 Division kuma kwamandan Operation Enduring Peace ya nuna damuwa kan harin, tare da bayar da umarnin gano wadanda suka aikata laifin.

Ya ce an fara bincike, tare da kira ga iyalan wadanda abin ya shafa da su kwantar da hankalinsu yayin da hukumomin tsaro ke kokarin cafke wadanda ke da hannu a lamarin.

Wannan hari na zuwa ne a daidai lokacin da ake kira ga kara tsaurara matakan tsaro a jihar Filato, wadda ta dade tana fama da rikice-rikicen da ke tsakanin manoma da makiyaya, musamman a Barkin Ladi da sauran kananan hukumomin makwabta.

Hukumomi sun sha alwashin kawo karshen rikice-rikicen, yayin da al’ummomi ke ci gaba da bukatar a tabbatar da tsaro da adalci mai dorewa.

Comments (0)
Add Comment