Wasu ’yan bindiga sun yi garkuwa da mai unguwar ƙauyen Kogari da ke Ƙaramar Hukumar Matazu a Jihar Katsina, Alhaji Bello Abdulkadir, yayin da yake cikin zaman jimamin rasuwar mai ɗakinsa.
Rahotanni sun ce maharan sun kuma yi awon gaba da wasu mata huɗu a harin da suka kai ƙauyen a daren Talata lokacin Sallar Isha’i.
Shaidu sun bayyana cewa maharan sun shiga ƙauyen ne sanye da kayan sojoji, inda suka fara harbe-harbe kafin su nufi gidan mai unguwar kai tsaye.
Mazauna yankin sun zargi yaran wani ƙasurgumin jagoran ’yan bindiga mai suna Muhammadu da hannu a harin, wanda ake zargin yana addabar yankunan Matazu da kewaye.
Rahotanni sun ƙara da cewa maharan sun kwashe kusan mintuna 45 suna cin karensu babu babbaka a ƙauyen, inda suka fasa shagunan cajin waya tare da sace wayoyi da sauran kayayyaki masu daraja.
Sabon harin ya sa mata da ƙananan yara da dama sun fara barin ƙauyen saboda fargabar sake kai wani farmaki, yayin da mazauna yankin ke kira ga gwamnati da ta ƙara tura jami’an tsaro domin kare rayuka da dukiyoyinsu.
Mai magana da yawun rundunar ’yan sandan Jihar Katsina, Sadiq Aliyu, ya ce zai yi karin bayani bayan kammala bincike kan lamarin.