’Yan Bindiga Sun Sace Matar Shugaban APC da Ɗansa a Kebbi

Yan bindiga sun sace matar da ɗan shugaban jam’iyyar APC na ƙaramar hukumar Yauri a jihar Kebbi, Yusuf Sani Alhassan.

Rahotanni sun nuna cewa lamarin ya faru ne a ranar Talata, lokacin da maharan suka kutsa kai tare da yin awon gaba da matar shugaban jam’iyyar da ɗansa.

Mai magana da yawun rundunar ’yan sandan jihar Kebbi, SP Bashir Usman, ya tabbatar da faruwar lamarin ga manema labarai, inda ya bayyana cewa rundunar ta fara bincike tare da ɗaukar matakan da suka dace domin ceto waɗanda aka sace da kuma kamo masu hannu a harin.

Lamarin na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da fuskantar matsalolin rashin tsaro da hare-haren sace mutane domin neman kuɗin fansa a wasu sassan jihar Kebbi da yankin Arewa maso Yammacin Najeriya.

Comments (0)
Add Comment