Yan Kwankwasiyya sun shigar da ƙarar Kakakin Gwamnan Kano kan zargin ɓatanci a midiya

Ƙungiyar ‘Yan Kwankwasiyya ta shigar da ƙara a gaban kotu kan Kakakin Gwamnan Kano, Sanusi Bature Dawakin Tofa, bisa zargin yin kalaman ɓatanci ga jagororinta ta hanyar soshiyal midiya.

Haka kuma, ƙarar ta haɗa da Shugaban Matasan jam’iyyar APC, Salisu Yahaya Hotoro, da mashawarcin Gwamna kan yaɗa labarai, Ibrahim Adam, tare da Nuhu Dambazau, waɗanda ake zargi da hannu a yaɗa kalaman da ƙungiyar ta ce sun ɓata mata suna.

A cikin ƙarar, ‘yan Kwankwasiyya sun bayyana cewa kalaman da ake zargin waɗannan mutane da yi sun ƙunshi cin mutunci da ɓata suna ga manyan jagororinsu, lamarin da suka ce ya saɓa wa doka.

Ƙungiyar ta buƙaci kotu da ta ɗauki matakin da ya dace domin kare mutuncin mambobinta tare da hana ci gaba da yaɗa irin waɗannan kalamai a kafafen sada zumunta.

Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, waɗanda ake ƙara ba su fitar da wata sanarwa a hukumance kan zargin da ake musu ba.

Comments (0)
Add Comment