’Yan  Sanda A Cross River Sun Gano Gawarwaki Takwas A Ɗakin Ajiyar Gawa

Rundunar ’yan sandan  jihar Cross River ta ce ta gano gawarwaki takwas da suka ruɓe a wani ɗakin ajiyar gawa a yankin Isong Inyang, dake ƙaramar hukumar Akamkpa.

Rundunar ta bayyana cewa an gano gawarwakin ne a wani wurin da ake adana gawarwaki, bayan samun bayanan sirri daga jama’a da suka sa jami’an tsaro suka kai samame wurin domin bincike.

Kakakin ’yan sandan jihar, ASP Eitokpah Sunday, ya ce rundunar na mayar da martani ne ga rahotannin da suka bazu a kafafen yaɗa labarai dangane da gano gawarwakin a ranar 13 ga watan Fabrairun 2026.

Ya ƙara da cewa rundunar ta samu sahihan bayanai da misalin ƙarfe 11:56 na safe, inda nan take jami’ai suka garzaya wurin domin tabbatar da sahihancin rahoton.

Da isarsu wurin, jami’an sun gano gawarwaki takwas da suka bushe a cikin ɗakin ajiyar gawarwakin, lamarin da ya jawo fara bincike domin gano yadda aka kai ga wannan hali.

’Yan sandan sun kuma kama wani mutum mai suna Sunday Ben Reuben, wanda ake zargi ma’aikaci ne a ɗakin ajiyar gawarwakin, kuma a yanzu haka yana hannun jami’an tsaro ana ci gaba da bincike a kansa.

Rundunar ’yan sandan ta buƙaci jama’a su kwantar da hankalinsu, tare da yin alƙawarin cewa za ta ci gaba da sanar da jama’a duk wani sabon bayani da aka tabbatar dangane da lamarin.

Comments (0)
Add Comment