Rundunar ƴan sandan Najeriya tare da haɗin gwiwar Cibiyar Yaƙi da Laifukan Intanet ta Ƙasa (NPF–NCCC) sun bayyana cewa sun bankaɗo wata babbar ƙungiyar masu satar katin waya ta intanet da ta haddasa asarar kuɗi da ta haura naira biliyan 7.7.
Rundunar ta bayyana hakan ne ta shafinta na X, inda ta ce ƙungiyar na karkatar da katin waya da bayanan intanet na wani kamfanin sadarwa ta hanyoyi ba bisa ka’ida ba.
Hakan ya biyo bayan ƙorafin da wani kamfanin sadarwa a Najeriya ya shigar, bayan da ya lura da ayyukan zamba da ba a amince da su ba a tsarin biyan kuɗaɗe da lissafin kuɗaɗensa. Binciken ƴan sanda ya nuna cewa an sace bayanan wasu ma’aikatan kamfanin ne, lamarin da ya bai wa masu laifin damar shiga muhimman tsarin kamfanin ba tare da izini ba.
Bayan shafe makonni ana gudanar da shiri da bincike, ƴan sanda sun kai samamen kama mutane a jihohin Kano da Katsina a watan Oktoban 2025, tare da kama wasu ƙarin da ake zargi a Babban Birnin Tarayya, Abuja.
A yayin samamen, an kama mutum shida da ake zargi da hannu a wannan laifi. Kayayyakin da aka ƙwato daga hannunsu sun haɗa da gidaje biyu a Kano, ƙananan kantuna biyu, da kuma shagunan sayar da wayoyi da kwamfutoci da ke ɗauke da sama da kwamfutoci 400 da wayoyi 1,000.
Haka kuma, ƴan sanda sun gano kuɗaɗe masu yawa a asusun bankin waɗanda ake zargin, kuɗaɗen da rundunar ke zargin an same su ne ta hanyar aikata wannan laifin.
Rundunar ƴan sanda ta ce za a gurfanar da waɗanda ake zargin a gaban kotu bayan kammala bincike, tare da tabbatar da cewa za ta ci gaba da yaƙi da laifukan intanet a faɗin ƙasar.