‘Yan Sanda Sun Cafke Wani Da Ake Zargi da Kashe Jami’an Tsaro a Jihar Benue

Rundunar ’yan sandan jihar Benue ta sanar da kama wani mutum da ake zargi da hannu a kashe-kashen jami’an tsaro a yankin Sankera da sauran sassa na jihar.

A wata sanarwa da rundunar ta fitar, ta ce an cafke wanda ake zargin, Yongu Justine Makwagh, ɗan ƙauyen Kadarko a jihar Nasarawa, da misalin ƙarfe 8 na dare a unguwar Balcony Park, Makurdi, bayan dogon bincike da leƙen asiri da rundunar ta gudanar.

Rundunar ta bayyana cewa Makwagh na cikin jerin mutanen da ta dade tana nema saboda rawar da ake zargin ya taka wajen kai hare-haren da suka yi sanadiyyar mutuwar jami’anta na Safer Highway Police a Yelwata, da kuma jami’an Department of Operations (DOPS) a Daudu, inda ake zargin sun kwace makamai daga hannun jami’an.

Kwamandan sashin Daudu tare da tawagar Intelligence Response Team (IRT) ne suka jagoranci bindiddigin wanda ake zargin, har ta kai ga an kama shi.

A halin yanzu, ’yan sanda sun ce ana ci gaba da bincike domin bankado sauran abokan aikinsa, tare da ƙoƙarin gano makaman da aka sace.

Rundunar ta ayyana wannan nasara a matsayin muhimmin mataki wajen dakile ayyukan ’yan bindiga da ke addabar jihar Benue da maƙwabtanta.

Comments (0)
Add Comment