Rundunar ’Yan Sandan Jihar Zamfara ta kama wata mota da ke ɗauke da abubuwan fashewa guda 954, waɗanda ake zargin an shirya kai su ga ’yan ta’adda domin kera bama-bamai. An kama direban motar, Mustapha Mohammad, mai shekaru 38, a wani samame da jami’an yaki da hakar ma’adinai ba bisa ka’ida ba suka gudanar bayan samun sahihan bayanan sirri.
Mai magana da yawun rundunar, Yazid Abubakar, ya ce an gano kayan ne a ranar 27 ga Janairu yayin binciken wata Toyota Corolla a Zamfara, inda aka ɓoye abubuwan cikin buhunan roba. Ya ƙara da cewa binciken farko ya nuna kayan na da alaƙa da ayyukan ta’addanci.
Rundunar ta ce ana ci gaba da bincike domin gano asalin kayan, inda aka nufa da su, da kuma duk wasu da ke da hannu a lamarin, yayin da aka mika abubuwan fashewar ga sashen kula da bama-bamai domin ƙarin bincike da ajiyewa.