Rundunar ’yan sandan Jihar Adamawa ta kama wasu mata biyu da ake zargi da safarar ƙananan yara, tare da ceto wasu ‘yan mata uku masu shekaru ƙasa da 18 a birnin Yola.
Mai magana da yawun rundunar, SP Suleiman Nguroje, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Laraba.
Ya ce jami’an Sashen Bayanai na Sirri na rundunar sun samu sahihan bayanai, wanda ya sa suka kai samame a tashar mota ta Adamawa Sunshine Motor Park a ranar 17 ga Fabrairu, 2026, inda suka tare ‘yan matan uku.
Nguroje ya bayyana sunayen ‘yan matan da aka ceto da Naomi Linus mai shekaru 14, Agnes Thomas mai shekaru 16, da kuma Patience Justine mai shekaru 15.
Binciken farko da ’yan sanda suka gudanar ya nuna cewa an yaudari ‘yan matan ne da alkawarin samar musu da aiki, inda aka kawo su Yola da nufin tura su zuwa Abuja domin aikin gida.
’Yan sandan sun bayyana sunayen matan da ake zargi da aikata laifin da Hasiya Yuguda mai shekaru 35, mazauniyar yankin NEPA a Jimeta, da Ummulkhairi Abubakar mai shekaru 40, mazauniyar Wuro-Hausa a Yola ta Kudu.
Sanarwar ta kuma ce wani mutum mai suna Simon Boniface mai shekaru 38 daga ƙaramar hukumar Zing a Jihar Taraba, yana taimaka wa ’yan sanda da bayanai yayin da bincike ke ci gaba.
A halin yanzu, an ajiye ‘yan matan da aka ceto a wuri na musamman, yayin da ake ƙoƙarin gano iyayensu domin mayar da su gida lafiya.
Kwamishinan ’yan sandan jihar, Morris Dankwambo, ya jaddada kudirin rundunar na yaƙi da safarar yara da kuma cin zarafin su, tare da kira ga jama’a da su rika sanar da hukumomi duk wani abu da suka gani mai kama da laifi da ya shafi ƙananan yara.
Wannan lamari na zuwa ne watanni kaɗan bayan gwamnatin Jihar Adamawa ta haɗa wasu yara da aka yi safarar su, tare da gargadin iyaye su rika kula da ‘ya’yansu, musamman wajen tafiye-tafiye ba tare da kulawa ba.