‘Yan sanda sun kama matashi kan yunkurin kashe masoyiyarsa a Gombe

Rundunar ‘yan sandan Jihar Gombe ta kama wani matashi mai shekaru 35 bisa zargin kai hari gidan wata matashiya da ake kyautata zaton masoyiyarsa ce, inda ya yi ƙoƙarin kashe ta tare da sace mata kuɗi.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, DSP Buhari Abdullahi, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar ga manema labarai.

A cewarsa, lamarin ya faru ne a unguwar Riyal da ke cikin birnin Gombe da misalin ƙarfe 2:00 na dare, lokacin da wanda ake zargin ya haura gidan matar.

Sanarwar ta ce da zarar ya shiga gidan, ya fara kai mata hari da guduma, tare da ƙoƙarin shaƙe wuyanta da wayar caja domin halaka ta.

Bayan kai harin, wanda ake zargin ya kwashe tsabar kuɗi har Naira 100,000 mallakin matar kafin ya yi yunƙurin tserewa daga wurin.

Sai dai matar ta samu damar yin kururuwar neman taimako, lamarin da ya jawo hankalin maƙwabta tare da tilasta wanda ake zargin tserewa daga gidan.

DSP Buhari Abdullahi ya ce bayan samun rahoton faruwar lamarin, jami’an ‘yan sanda suka fara bincike wanda ya kai ga cafke wanda ake zargin.

Ya ƙara da cewa rundunar na ci gaba da gudanar da bincike domin gano cikakken abin da ya faru, kafin gurfanar da wanda ake zargin a gaban kotu domin fuskantar hukunci.

Comments (0)
Add Comment