’Yan Sanda Sun Kama Mutane Biyu da Suka Yi Barazanar Garkuwa da Wani Mutum a Adamawa

Rundunar ’Yan Sanda a Jihar Adamawa ta kama wasu mutane da ake zargi da kiran wani ta waya suka yi masa barazanar garkuwa da kashe shi idan bai biya kuɗi ba, a Karamar Hukumar Song.

Hakan na cikin wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na rundunar, SP Suleiman Yahaya Nguroje, ya fitar ranar Asabar, 22 ga Nuwamba 2025.

Sanarwar ta bayyana cewa jami’an tsaro sun cafke Ahmadu Alhaji Halilu da Adamu Buba Balejo tare da wasu da ake zargi, bayan bin diddigin lambar wayar da aka yi amfani da ita wajen yin barazanar.

Rundunar ta ce wadanda ake zargin sun amsa laifukan da ake tuhumar su da su, kuma za a mika su kotu da zarar an kammala bincike.

Comments (0)
Add Comment