‘Yan Sanda Sun Kama Tsohon Shugaban Jam’iyyar APC Na Jihar Jigawa

Jami’an ‘yan sanda sun kama tsohon shugaban jam’iyyar APC na jihar Jigawa, Alhaji Habibu Sani Sara, da wani jigo a jam’iyyar.

Wata majiya a hedikwatar ‘yan sandan ta tabbatar wa manema labarai cewa an gayyaci tsohon shugaban da daya jigon kuma an tsare su ne saboda korafin da wani Malam Habibu Muhammad Ringim, mai bawa gwamna shawara na musamman kan yada labarai ya shigar.

Ya ce wasu daga cikin korafe-korafen sun hada da bata sunan Gwamna Muhammad Badaru Abubakar a wani shiri na rediyo.

Kakakin rundunar ‘yan sandan, DSP Lawan Shiisu Adam, ya ce bayanan ba su isa teburinsa ba har ya zuwa lokacin hada wannan rahoton.

An rawaito cewa Habibu Sara da Habu Karami Jahun a yayin da suke gabatar da wani shiri a gidan rediyo, sun zargi Gwamna Badaru Abubakar da bada kwangiloli barkatai da ka iya zama alakakai ga magajinsa. Sun kuma zarge shi da yunkurin ci gaba da mulki har bayan ranar 29 ga watan Mayun 2023, ta hanyar nada kwamishinoni da wasu muhimman mukamai a gwamnatin Malam Umar Namadi mai jiran gado.

Comments (0)
Add Comment