‘Yan Sanda Sun Kwato Mota Da Aka Sace A Gwaram

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Jigawa ta kama wani mutum da ake zargi da satar mota kirar Hijet a karamar hukumar Gwaram ta jihar.

Jami’an rundunar sun ce sun samu nasarar cafke wanda ake zargin ne bayan gudanar da bincike da sintiri a yankin, inda aka kwato motar da ake zargin ya sata.

Rundunar ta bayyana cewa ana ci gaba da bincike domin gano ko akwai wasu mutane da suke da hannu a lamarin kafin gurfanar da wanda ake zargin a gaban kotu.

Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Jigawa, Haruna A. Yahaya, ya yaba wa jami’an rundunar bisa kokari da jajircewa wajen yaki da masu aikata laifuffuka, tare da kira ga jama’a su ci gaba da bayar da bayanan sirri domin taimakawa wajen tabbatar da tsaro a jihar.

Comments (0)
Add Comment