’Yan Sandan Yobe Sun Kama Wani Mutum da Ake Zargin Ya Kasha Abokinsa Saboda Yayi Hulɗa da Matarsa

Rundunar ’yan sandan Jihar Yobe ta tabbatar da cafke wani mutum mai shekaru 50, Alhaji Hassan Umaru, kan zargin kashe abokinsa.

Rahoton ya ce lamarin ya faru ne a ranar 1 ga Fabrairu, 2026, da misalin ƙarfe 12:30 na rana a ƙauyen Bundila da ke Karamar Hukumar Gulani.

Kakakin rundunar, SP Dungus Abdulkarim, ya bayyana cewa wanda ake zargin ya kai harin ne bayan ya zargi mamacin da yin hulɗa da matarsa.

’Yan sanda sun ce rikicin ya ɓarke ne a kasuwar ƙauyen, inda wanda ake zargin ya sari mamacin da adda.

An gaggauta kai wanda aka jikkata zuwa cibiyar lafiya ta Bularaba, inda likita ya tabbatar da rasuwarsa.

Rundunar ta ce an cafke wanda ake zargin nan take, tare da ƙwato addar da ake zargin an yi amfani da ita.

Kwamishinan ’yan sandan jihar, Emmanuel Ado, ya gargadi al’umma da su guji ɗaukar doka a hannu, tare da kira da a kai ƙorafi ga hukumomi idan irin haka ta faru.

Comments (0)
Add Comment