An tabbatar da mutuwar wani yaro dan shekara uku mai suna Abdura’uf Badamasi, bayan da ya fada cikin rijiya a kauyen Wangara da ke Karamar Hukumar Tofa a Jihar Kano.
Rundunar kashe gobara ta Jihar Kano ta ce ta samu kiran gaggawa da misalin karfe 7:50 na safiyar Juma’a, 30 ga watan Janairu, game da faruwar lamarin.
A cewar wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na hukumar, Saminu Yusif Abdullahi ya fitar, wani mai suna Dan Asabe Rabiu ne ya sanar da su abin da ya faru.
Sanarwar ta ce nan take aka tura tawaga daga hedkwatar hukumar zuwa inda lamarin ya faru domin daukar matakin gaggawa.
Da isarsu wurin, jami’an kashe gobara sun samu labarin cewa an dade ana neman yaron tun daren Alhamis, inda iyayensa ke zargin ya fada cikin wata rijiya a cikin kauyen.
Jami’an sun shiga cikin rijiyar suka fitar da yaron a sume, amma daga bisani aka tabbatar da rasuwarsa bayan an duba lafiyarsa.
Daga karshe, an mika gawar yaron ga hakimin unguwar Wangara bisa ka’idojin da aka tanada, yayin da hukumar kashe gobara ta mika sakon ta’aziyya ga iyalansa tare da kira ga jama’a da su rika rufe rijiyoyi domin kare lafiyar yara.