Yawan bashin da ke kan Najeriya ya kai naira triliyan 32

Ofishin kula da basussuka na Najeriya ya ce ya zuwa karshen watan Disambar shekarar bara ta 2020, yawan bashin da ke kan kasar ya kai Naira triliyan 32 da biliyan 915.

Sanawar da ofishin ya wallafa a shafinsa na Intanet ya ce bashin ya kunshi wanda ke kan gwamnatin tarayya, da na jihohi da kuma birnin Abuja.

Rahoton ya ce yawan basukan da ake bin Najeriya a matakin tarayya ya ragu sosai bayan da kasar ta fice daga matsin tattalin arziki a shekarar 2017.

A shekarar ta 2017 bashin da gwamnatin Najeriyar ta ciwo don cike gibin kasafin kusin kasar a matakin tarayya ya kai naira triliyan 2 da biliyan 300, a 2018 ya ragu zuwa naira triliyan 2, a shekarar 2019 ya sake raguwa zuwa naira triliyan 1 da biliyan 600, yayin da a 2020 a kudurin kasafin kudin shekarar da aka gabatar bashin da aka tsara ci ya ragu zuwa naira triliyan 1 da biliyan 5.

Sai dai a cewar rahoton, saboda barkewar annobar Korona da ta tagayyara tattalin arzikin mafi akasarin kasashe, bayan sake nazari kan kasafin kudin Najeriyar, an kara yawan bashin da za a ciwo don cike gibi zuwa naira triliyan 4.

TATTALIN ARZIKI
Comments (0)
Add Comment