Za a kafa sabon ofishin Hukumar Kiyaye Afkuwar Hadura a jihar Jigawa

Shugaban Hukumar Kiyaye Afkuwar Hadura ta Kasa Mista Boboye Oyeyemi, ya amince da kafa sabon reshen ofishin hukumar a karamar hukumar Ringim ta nan Jihar Jigawa.

Kwamandan Hukumar na Jihar Jigawa Malam Muhammad Ahmed, shine ya bayyana hakan a lokacin da ya ziyarci Mai Martaba Sarkin Ringim Alhaji Sayyadi Mahmoud Ringim, a fadarsa domin karfafa alaka da kuma girmamawa.

Malam Muhammad Ahmed, ya ce hukumar ta damu da yadda ake samun guje-guje a hanyar da kuma tukin ganganci a hanyar Hadejia, Ringim Kano wanda hakan ya haifar da asarar rayuka masu tarin yawa.

A cewarsa, sun kawo ziyarar ne domin girmama Sarkin Ringim tare da fada masa cigaba da aka samu wajen kafa sabon Ofishin Hukumar a Karamar hukumar wanda zai fara aiki.

Haka kuma ya ce sabon ofishin zai taimakawa hukumar wajen kaiwa daukin gaggawa a duk lokacin da hadarin mota ya auku.

Da yake mayarda jawabi Sarkin na Ringim, ya yabawa hukumar tare da bada tabbacin cewa taimakawa hukumar domin ganin cewa ta sauke nauyin da ya rataya a kanta.

Comments (0)
Add Comment