Za a samar da fanfunan burtsatse guda 270 ga al’ummar Fulani a jihar Jigawa

Kungiyar Fulani Miyatti Allah Kautal Hore ta kasa reshen Jihar Jigawa hadin gwiwa da ma’aikatar ruwa ta jiha, na shirin samar da fanfunan burtsatse ga al’ummar Fulani a rugage 270 zuwa farkon shekara mai kamawa.

Shugaban kungiyar na jiha Malam Umar Kabiru Dubantu Hadejia shine ya sanar da haka yayin fira da wakilinmu, Faruk Ahmad Kafin Haausa.

Comments (0)
Add Comment