Za’a kammala aikin gyaran matatar mai ta Kaduna a karshen shekarar 2024

Hukumar gudanarwar kamfanin man fetur ta kasa ta ce za a kammala aikin gyaran matatar mai ta Kaduna a karshen shekarar 2024 bayan shafe shekaru matatar tana rufe saboda rashin kulawa.

Manajan Daraktan matatar man ta garin Kaduna, Mustafa Sugungun ne ya bayyana haka a jiya Litinin a yayin ziyarar gani da ido da ya kai a matatar man tare da da ‘yan kwamitin majalisar dattawan kan harkokin man fetur karkashin jagorancin Sanata Ifeanyi Ubah.

Ya bayyana cewa matatar man da zata rika hako mai ganga 110,000 a kowace rana za ta fara samar da kashi 60 cikin 100 nan da karshen shekara, yayin da za a fara cikakken aikin matatar daga baya.

Shugaban matatar ta Kaduna ya bayyana cewa aikin gyaran da akayi a halin yanzu ya kai kashi 40 cikin 100, ana sa ran kammala aikin cikin wa’adin da aka kayyade.

Comments (0)
Add Comment