Zaman majalisar tattalin arzikin kasa bai tabo batun kafa ’yan sandan jihohi ba

A zaman majalisar tattalin arzikin kasa da aka gudanar a fadar shugaban kasa jiya Alhamis, mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima tare da gwamnoni da ministoci ba su tabo batun kafa ’yan sandan jihohi ba, duk da matsanancin rashin tsaro da ke addabar kasar.

Gwamnan Jihar Bayelsa, Douye Diri, ya bayyana cewa an kasa samun lokacin tattauna batun ne saboda yawancin gabatarwar da aka yi a taron, amma ya yi alkawarin za a duba batun sosai a taronsu na gaba.

Wannan shi ne karo na uku da majalisar ke jinkirta batun kafa ’yan sandan jihohi tun bayan da gwamnonin jihohi 36 suka mika ra’ayoyinsu, mafi yawa daga cikinsu na goyon bayan kafa rundunar.

A halin da ake ciki, Gwamnonin Najeriya sun kafa wani kwamitin riko da zai yi aiki tare da shugabannin hukumomin tsaro, yayin da rundunar soji ta ce ta kashe ‘yan ta’adda 1,770 a arewa maso yamma cikin shekaru uku, tare da kama wasu 3,070 da kwato makamai da harsasai fiye da 13,000.

A wani bangare na taron majalisar tattalin arzikin kasa, an yanke hukunci cewa ya zama dole a canja tsarin kiwon dabbobi daga na gargajiya zuwa na zamani domin magance rikicin manoma da makiyaya.

Gwamna Douye Diri na Bayelsa ne ya bayyana hakan ga manema labarai, inda ya ce tsarin kiwon yanzu yana haddasa rikici da asarar rayuka kamar yadda aka gani a jihohin Benue, Plateau da Kwara.

Ya kara da cewa sabuwar ma’aikatar kiwon dabbobi ta bullo da tsari na bunkasa kiwo da ke nufin samar da kudin shiga har dala biliyan 90 nan da shekarar 2035.

Rahotanni sun nuna cewa rikicin fili tsakanin manoma da makiyaya na da nasaba da karancin fili da dumamar yanayi, da kuma rashin tabbataccen tsari daga bangaren gwamnati, wanda hakan ke haddasa ramuwar gayya marasa iyaka.

Comments (0)
Add Comment