Shugaban Majalissar Kasuwancin Najeriya da Turkiyya, Dele Oye, ya bayyana manufar ziyarar Shugaba Bola Tinubu zuwa Turkiyya.
Da yake magana a wata hira da tashar Arise Television a shirin “Morning Show,” Oye ya ce ziyarar na da nufin sabunta dangantakar kasuwanci tsakanin kasashen biyu.
Ya ce ziyarar Tinubu ta kara karfafa alakar kasashen biyu tare da taimakawa wajen magance manyan kalubalen tsaro da sauran batutuwan hadin gwiwa.
Oye ya kara da cewa a hukumance, cinikayya tsakanin Najeriya da Turkiyya tana tsakanin dala biliyan 1 zuwa 2, yana mai cewa kayayyakin Turkiyya suna kusan a kowanne gida a Najeriya.
Ya kuma bayyana cewa ba a hukumance ba, yawan cinikayyar na iya wuce dala biliyan 10. Ya kara da cewa rattaba hannu kan yarjejeniyoyin fahimtar juna (MoU) zai kara wa ‘yan kasuwar Najeriya damar hada gwiwa da takwarorinsu na Turkiyya.
A cewarsa, “Ziyarar Shugaba Tinubu babbar nasara ce ga Najeriya. A halin yanzu, cinikayya tsakanin kasashen biyu tana kusan dala biliyan 1 zuwa 2, kuma kusan babu gidan da ba za ka samu kayan Turkiyya ba a Najeriya. Saboda haka akwai bukatar a sabunta wannan alaka, kuma rattaba hannu kan wadannan yarjejeniyoyi zai kara mana karfin ci gaba da kasuwanci da Turkiyya.”