Ƙungiyar Amnesty International ta nemi a dakatar da kamfanin Shell daga hakar mai a yankin Neja Delta

Ƙungiyar kare haƙƙin ɗan adam ta Amnesty International ta shiga sahun masu kira ga gwamnatin tarayya da ta dakatar da kamfanin mai na Shell daga gudanar da aikinsa a ƙasar har sai an samar da kariya ga mutanen Neja Delta. Ƙungiyar ta ce ayyukan kamfanin na ƙara haifar da cin zarafin ɗan adam idan har ba a shawo kan matsalar gurɓata muhalli da kamfanin ke haifarwa ba. Ƙungiyar ta ce dole ne kamfanin ya samar da wadatattun kuɗin da za a yi amfani da su wajen gyara gurɓacewar muhalli da ayyukansa ya janyo sannan dole a tuntuɓi mutanen yankin kan maganar sayar da kamfanin kan fiye da dala biliyan 2.4. Masu fafutuka sun zargi Shell da hannu wajen yawan malalar mai a yankin Neja Delta da wasu matsalolin da suka janyo gurbacewar magudanan ruwa. Gwamnatin tarayya dai ba ta ce komai ba kan batun. A baya kamfanin na Shell, ya yi alƙawarin sabbin mamallaka kamfanin za su duba ɓarnar da aka yi.

Comments (0)
Add Comment