Ƴan Najeriya za su fara neman rigakafin corona domin su saya da kuɗinsu amma su rasa a cewar Sarkin Dutse

Mai Martaba Sarkin Dutse, Dr. Nuhu Muhammad Sanusi, yayi gargadin cewa akwai yiwuwar nan gaba kadan ‘yan Najeriya za su fara neman rigakafin corona domin su saya da kudinsu amma su rasa.

Sarkin ya sanar da haka yayin kaddamar da gangamin rigakafin corona a karamar hukumar Kiyawa.

Sarkin, wanda ya samu wakilcin babban dan majalisar sarki, Galadiman Dutse, Alhaji Basiru Muhammad Sanusi, ya bukaci ‘yan Najeriya da su fito kwansu da kwarkwata domin ayi musu rigakafin.

Ya bukaci ‘yan kasarnan da su tallafawa kokarin gwamnati da abokan hulda na cigaba, wajen dakile bazuwar kwayar cutar ta hanyar amincewa ayi musu rigakafin.

Sarkin, daga nan ya umarci dukkan hakiman dake kasarsa, da shugabannin addinai, da su marawa aikin rigakafin corona baya, domin cimma burin da aka sanya a gaba.

Comments (0)
Add Comment