An bukaci yayan jam’iyyar NNPP na jihar Jigawa da su kasance masu biyayya ga dokokin jam’iyyar na kasa

Am bukaci yayan jam’iyyar NNPP mai kayan dadi dake fadin kasar nan da su kasance masu biyayya ga dokokin jam’iyyar.

Mataimakin shugaban jam’iyyar na shiyyar Arewa maso yamma kuma guda cikin Yan kwamitin uwar jam’iyyar na kasa Honourable Abdul’aziz Usman Tarabu ne yayi wannan kiran a lokacin da ake gudanar da zaben fidda gwani na dan takarar kujerar majalissar dokoki ta kasa mai wakiltar kananan hukumomin Guri, Birniwa da Kirikasamma.

Usman Tarabu ya kuma yabawa yayan jam’iyyar bisa kokarin da suka nuna wajan gudanar da zaben fidda gwamni na jam’iyyar da aka gudanar.

Yayin dayake ya bayyana wanda ya lashe zaben fidda gwanin, Jami’in tattara sakamakon zaben wanda akak turo daga hedikwatar jam’iyyar na jiha Muhammad Saleh Hadejia.

Yace bayyana Adamu Hassan Abunabu a matsayin wanda ya lashe zaben fidda gwanin, bayan ya samu kuru’u 68.

Yayin dayake jawabinsa bayan samun nasarar Alhaji Adamu Hassan Abunabu ya godewa Deligates na jam’iyyar, tare da alkawarin yin aiki tukuru domin samun nasara.

Comments (0)
Add Comment