An hana tsohon mataimakin gwamnan Kano, Nasiru Yusuf Gawuna, da Aminu Abdussalam shiga gidan jagoran jam’iyyar NDC na ƙasa, Seriake Dickson, domin tattaunawa kan rikicin tsayar da ‘yan takara a Jihar Kano.
Majiyoyi daga gidan Dickson na cewa lamarin ya faru ne a daren Lahadi, lokacin da wakilan Sanata Rabiu Musa Kwankwaso suka isa gidansa da ke Abuja domin ganawa da shi kan rikicin da ya shafi rabon takara a jam’iyyar.
Rahotanni sun ce an sanar da su cewa Dickson ya bayar da umarnin kada a bari su shiga gidan, domin ba ya son ganawa da su a wannan lokaci.
Lamarin na zuwa ne yayin da ake ci gaba da takaddama kan tsarin rabon takara na kashi 60 da 40 tsakanin ‘yan Kwankwasiyya da kuma ‘yan tsohuwar NDC a Jihar Kano.