An hana Gawuna da Kwamared Aminu shiga gidan jagoran NDC na kasa kan batun tsayar da ‘yan takarar jihar Kano
An hana tsohon mataimakin gwamnan Kano, Nasiru Yusuf Gawuna, da Aminu Abdussalam shiga gidan jagoran jam’iyyar NDC na ƙasa, Seriake Dickson, domin tattaunawa kan rikicin tsayar da ‘yan takara a Jihar Kano.
Majiyoyi daga gidan Dickson na cewa lamarin ya faru ne a daren Lahadi, lokacin da wakilan Sanata Rabiu Musa Kwankwaso suka isa gidansa da ke Abuja domin ganawa da shi kan rikicin da ya shafi rabon takara a jam’iyyar.
Rahotanni sun ce an sanar da su cewa Dickson ya bayar da umarnin kada a bari su shiga gidan, domin ba ya son ganawa da su a wannan lokaci.
Lamarin na zuwa ne yayin da ake ci gaba da takaddama kan tsarin rabon takara na kashi 60 da 40 tsakanin ‘yan Kwankwasiyya da kuma ‘yan tsohuwar NDC a Jihar Kano.