Gwamna Makinde Ya Sanya Hannu Kan Dokar Hana Achaba A Oyo

0 175

Seyi Makinde ya rattaba hannu kan dokar hana amfani da baburan haya (achaba) a wasu sassan Jihar Oyo, a wani mataki da gwamnatin jihar ta ce an ɗauka ne domin ƙara inganta tsaro.

Matakin ya zo ne bayan wasu hare-hare da suka haɗa da sace ɗalibai da malamansu a ƙaramar hukumar Orire, lamarin da ya tayar da hankalin al’umma kan buƙatar ƙarin matakan tsaro.

Gwamnatin jihar ta bayyana cewa dokar na da nufin rage amfani da babura wajen aikata laifuka da kuma taimakawa jami’an tsaro wajen sa ido da kare rayuka da dukiyoyin al’umma.

Sai dai matakin ya janyo ra’ayoyi mabambanta, inda wasu ke ganin zai taimaka wajen magance matsalar tsaro, yayin da wasu masu sana’ar achaba ke nuna damuwa kan yadda dokar za ta shafi hanyoyin samun abincinsu.

Leave a Reply