Gwamnatin Bangladesh ta hana a yi layya da bijimin da ake wa laƙabi da Donald Trump

0 406

Wani bijimi da ya shahara a Bangladesh sakamakon kamanceceniyar da ake ganin yana da ita da Shugaban Amurka, Donald Trump, ya tsallake rijiya da baya, bayan gwamnatin ƙasar ta hana a yi layya da shi tare da mayar da shi gidan Zoo.

Bijimin, wanda jama’a suka yi wa laƙabi da “Donald Trump”, ya jawo hankalin mutane da dama saboda farin launin fuskarsa da kuma gashin kansa mai ruwan gwal da ya zubo a saman goshinsa, abin da wasu ke ganin ya yi kama da salon gashin shugaban Amurka.

Lamarin ya haddasa cece-kuce a kafafen sada zumunta da kuma faɗin ƙasar, inda mutane da dama suka riƙa tururuwa domin ganin bijimin da idonsu.

Bayan shahararsa ta ƙaru da kuma yawan masu zuwa kallonsa, gwamnatin Bangladesh ta ɗauki matakin hana a yi layya da shi bana, tare da mayar da shi wani gidan Zoo domin kare shi.

Matakin ya sa bijimin ya tsallake yanka a lokacin bukukuwan Babbar Sallah, yayin da yake ci gaba da jan hankalin masu ziyara da ke tururuwa domin ganinsa.

Rahotanni sun ce bijimin ya zama abin kallo da tattaunawa a sassa daban-daban na ƙasar, inda wasu ke ɗaukarsa a matsayin wani abin al’ajabi saboda kamanninsa da shugaban Amurka.

Leave a Reply