Home Archive by category Labarai

Labarai

Labarai

Yadda yan IPOB suka kashe ‘yan Arewa 10 ciki har da mace mai juna biyu da ‘ya’yanta 4 da wasu mutane 6 a jihar Anambra

‘Yan haramtacciyar kungiyar IPOB masu fafutukar kafa kasar Biafra, a ranar Lahadi sun kashe ‘yan Arewa 10, ciki har da mace mai juna biyu, da ‘ya’yanta 4 da wasu mutane 6 a kauyen Isulo dake karamar hukumar Orumba ta Arewa a jihar Anambra. An bayyana sunan matar da aka kashe da Harira Jibril Continue reading
Labarai

Sama da mutane 30 ne aka ruwaito sun bace a jihar Borno bayan da wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne suka kai musu hari

Sama da mutane 30 ne aka ruwaito sun bace a jihar Borno bayan da wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne suka kai musu hari a karshen mako. Shaidu sun ce ‘yan bindiga ne a kan babura suka yi wa mutanen garin luguden wuta a lokacin da suka shiga daji domin dibar itace. A cewar […]Continue reading
Labarai

Tsohon gwamnan jihar Gombe, Ibrahim Dankwambo, ya karbi tikitin takarar Sanatan Gombe ta Arewa domin tsayawa takara a jam’iyyar PDP a 2023

Tsohon gwamnan jihar Gombe, Ibrahim Dankwambo, a jiya ya karbi tikitin takarar Sanatan Gombe ta Arewa domin tsayawa takara a jam’iyyar PDP a 2023. Habu Zarma, wanda shi ne jami’i mai kula da zaben, ya ce Dankwambo ya samu tikitin ne biyo bayan janyewar sauran ‘yan takara biyu, tsohon mataimakin kakakin majalisar wakilai, Usman Bayero […]Continue reading
Labarai

Yadda Ibrahim Saminu Turaki ya kasance dan takarar sanata mai wakiltar mazabar Jigawa ta Arewa maso Yamma – PDP

A jiya ne aka zabi tsohon gwamnan jihar Jigawa, Ibrahim Saminu Turaki a matsayin dan takarar sanata na jam’iyyar PDP mai wakiltar mazabar Jigawa ta arewa maso yamma. Saminu Turaki wanda ya koma jam’iyyar PDP kwanan nan ya ci zabe babu hamayya a zaben da ya gudana a karamar hukumar Gumel. Haka kuma, an zabi […]Continue reading
Labarai

Ma’aikatar kula da muhalli ta jihar Jigawa ta yi barazanar daukar mataki akan wanda aka samu da laifin cin iyakar makiyaya

Ma’aikatar kula da muhalli ta jihar Jigawa ta yi barazanar daukar mataki akan wanda aka samu da laifin cin iyakar makiyaya tare da kutse a dajin gwamna da kuma sare bishiya ba bisa ka’ida ba. Kwamishinan ma’aikatar, Alhaji Ibrahim Baba Chaichai, ya yi wannan gargadi lokacin da ya ziyarci garuruwan Kwari da Safa da Kumbura […]Continue reading
Labarai

Fiye da mutum 20 sun mutu sakamakon wata gagarumar ambaliyar ruwa a kasar Indiya

Ambaliyar ruwa ta janyo zabtarewar kasa a arewa maso gabashin jihar Assam da ke Indiya, tare da hallaka mutum 25, wasu 65,000 kuma suka tsere daga gidajensu. A ranar Talata ne jami’ai a jihar suka ce kwanaki goma ke nan ana tafka ruwan sama mai karfin gaske, kuma da ma can jihar Assam na fama […]Continue reading
Labarai

Masu bukata ta musamman sun yi barazanar kai karar INEC kotu bisa rashin samar da abubuwan da suke bukata na zabe

Masu bukata ta musamman a jihar Ekiti da ke kudancin Najeriya sun yi barazanar kai hukumar zabe mai zaman kanta INEC gaban kuliya, kan korafin kin tanadar abubuwan da suke bukata domin shiga zaben gwamna da za a yi a jihar ranar 18 ga watan Yuni. Jaridar Premium Times ta ambato shugaban kungiyar masu bukata ta musamman […]Continue reading
Labarai

Rundunar ‘yan sandan jihar Jigawa ta gargadi matasa da su guji duk wani abu da zai kawo cikas ga zaman lafiya da ake samu a jihar

Rundunar ‘yan sandan jihar Jigawa ta gargadi matasa da su guji duk wani abu da zai kawo cikas ga zaman lafiya da ake samu a jiharnan. A wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar, Lawan Shiisu Adam ya fitar, ya ce gargadin ya zama wajibi biyo bayan tashin hankalin da wasu fusatattun matasa ke […]Continue reading
Labarai

Hukumar EFCC ta sake gurfanar da Sambo Dasuki da tsohon gwamna Attahiru Bafarawa da tsohon ministan kudi Bashir Yaguda da wasu mutane biyu bisa zargin karkatar da kudi naira miliyan dubu 23 da miliyan 300

Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati, EFCC, a jiya ta sake gurfanar da Kanar Sambo Dasuki mai ritaya, da tsohon gwamna Attahiru Bafarawa, da tsohon ministan kudi, Bashir Yaguda, da wasu mutane biyu, bisa zargin karkatar da kudi naira miliyan dubu 23 da miliyan 300. Sauran wadanda aka gurfanar sun hada da […]Continue reading
Labarai

Gwamnatin jihar Bauchi ta amince da ware kudi naira miliyan 15 domin shiryawa domin yakar cutar kumburin ciki

Gwamnatin jihar Bauchi ta amince da ware kudi naira miliyan 15 domin shiryawa domin yakar cutar kumburin ciki, amai da gudawa, da sauran cututtuka a jihar. Babban Sakataren Hukumar Kula da Lafiya a matakin farko ta Jihar Bauchi, Dokta Rilwanu Mohammed ne ya bayyana haka a jiya a wata hira da Kamfanin Dillancin Labarai na […]Continue reading