Jam’iyyar PDP a jihar jigawa ta tsayar da ranar gudanar da taron kananan hukumomi a jihar

0 204

Jam’iyyar PDP a jihar jigawa ta tsayar da ranar 27 ga Yuli, domin gudanar da taron kananan hukumomi a jihar.

Shugaban jam’iyyar PDP na jihar Jigawa, Ali Diginsa ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya raba wa manema labarai a jiya Lahadi.

Ya bayyana cewa jam’iyyar tana nan daram kuma ta shirya tsaf don halartar taron kananan hukumomi da aka shirya gudanarwa a ranar 27 ga Yuli 2.

A cewarsa, Bayan sabunta rijistar mambobinta a sassan kasar 287, jam’iyyar ta gudanar da taron masu ruwa da tsaki a dukkan matakai.

Ya ce suna da  kyaky-kyawan shugabanci a jihar Jigawa, kuma mu ‘yan PDP masu bin doka da oda ne a Jigawa da  ma kasa baki daya.

Leave a Reply

%d bloggers like this: