Gwamna jihar Kano Abba Kabir Yusuf, ya ba wa mazauna jihar tabbacin shirin gwamnatinsa na gudanar da zaben kananan hukumomi.
Da yake tabbatar da hakan ta wata sanarwa, mai magana da yawun gwamnan, Sanusi Tofa, ya ce gwamnan ya bayyana hakan ne a yayin wani taron masu ruwa da tsaki da shugabannin jam’iyyar NNPP mai mulki a gidan gwamnatin jihar Kano.
Bugu da kari, gwamnan ya bayyana shirin gudanar da zaben kansilolin bisa ga hukuncin da kotun koli ta yanke, inda ya tabbatar da ‘yancin cin gashin kan kananan hukumomi a matsayin mataki na uku na gwamnati.
A cikin sanarwar Gwamnan ya tabbatar da mutunta doka da kuma jajircewar sa na yin taka-tsan-tsan a harkokin kudi, rikon amana da kuma nuna gaskiya a harkokin mulki a dukkan matakai.
Sanarwar ta ce, shirye-shiryen da hukumar zabe mai zaman kanta ta jihar Kano ke yi na gudanar da zabukan kansiloli.