An yi nasarar tarwatsa tare da lalata sansanin ‘yan ta’adda masu fafutukar kafa kasar Biafra

0 181

Rundunar sojin kasar ta ce dakarunta sun yi nasarar tarwatsa tare da lalata sansanin ‘yan ta’adda  masu fafutukar kafa kasar Biafra, IPOB da kuma kungiyar tsaro ta Gabas, ESN.

Rundunar, a wani sako da ta wallafa a shafinta na X- a ranar Asabar, ta ce an gudanar da aikin ne da sanyin safiyar ranar a dajin Ezere da ke Umuawa Aku, a karamar hukumar Okigwe ta Imo.

Ta ce sojojin da ke aiki da bayanan sirri game da muzgunawa da kuma tsoratar da mazauna yankin da ‘yan ta’adda ke yi, sun yi gaggawar yin shiri don kawar da barazanar.

A cewar sanarwar, sojojin da suka isa wurin, sun yi artabu da ‘yan ta’addan, inda suka fatattake su daga sansaninsu.

Ya kara da cewa sojojin sun yi amfani da nasarar da suka samu, lamarin da ya tilasta musu yin watsi da tarin makaman su.

Leave a Reply

%d bloggers like this: