An Kama Jami’in DSS Na Bogi A Abuja

0 73

An kama jami’in DSS na bogi a Abuja

Hukumar Tsaron Farin Kaya (DSS), ta kama wani mutum mai suna Moferewa Maiye bisa zargin yin ƙaryac cewa shi jami’in hukumar ne.

An kama Maiye ne a maɓoyarsa da ke kusa da mahadar NITEL, a kan titin Adetokunbo Ademola Way, Wuse II, Abuja.

A lokacin da aka kama shi, yana sanye da kayan aiki na DSS kuma yana ɗauke da bindigar bogi.

Wata majiyar tsaro ta ce jami’an DSS sun samu bayanin cewa Maiye yana amfani da kayan da bindigar bogi wajen tsoratar da direbobi da sauran jama’a tare da karɓar kuɗi a hannunsu.

A yayin bincike, Maiye ya ce kayan DSS da ke hannunsa na ɗan uwansa da ya rasu mai suna Monday Maiye, wanda ya ce tsohon jami’in DSS ne.

DSS na ci gaba da bincike domin gano yadda wanda ake zargin ya samu kayan hukumar da kuma tsawon lokacin da ya kwashe yana damfarar jama’a.

Lamarin ya ƙara jawo hankalin hukumar kan mutanen da ke fakewa da sunan jami’an tsaro domin tsoratar da jama’a da aikata laifuka.

Leave a Reply