Davido Aka So Kashewa A Harin da Aka Kai Wa Tawagar Adeleke — ’Yan Sanda

0 62

Davido aka so kashewa a harin da aka kai wa tawagar Adeleke — ’Yan Sanda

Fitaccen mawaƙin Kudancin Najeriya, David Adeleke, wanda aka fi sani da Davido, shi aka so a farmaka a lokacin da aka kai wa tawagar Gwamnan Jihar Osun, Ademola Adeleke hari, kamar yadda ’yan sanda suka bayyana.

Lamarin ya faru ne a Osogbo a ranar Laraba lokacin da gwamnan ya ziyarci fadar Ataojan Osogbo, bayan ya karɓi takardar shaidar lashe zaɓe daga hukumar INEC.

Davido, wanda ɗan uwan gwamnan ne, yana cikin mutanen da suka raka shi.

Mazauna yankin sun ce harbe-harbe ya jefa jama’a cikin firgici na tsawon minti 15, yayin da jami’an tsaron gwamnan suka yi musayar wuta da maharan ne.

Kakakin rundunar ’yan sandan Jihar Osun, Abiodun Ojelabi, ya ce bincikensu ya nuna cewa wasu da ake zargin maharan wata ƙungiya ne suka yi ƙoƙarin kai wa Davido hari, amma jami’an tsaronsa suka daƙile su.

Lamarin ya rikiɗe zuwa musayar wuta.

Wani mutum mai shekaru 60 mai suna Tajudeen Yusuf, ya samu rauni kuma daga bisani ya mutu a asibiti.

’Yan sanda sun ce sun fara gudanar da cikakken bincike kuma suna ƙoƙarin cafke waɗanda ake zargi da hannu a harin.

Sun kuma buƙaci jama’a su kwantar da hankalinsu tare da bayar da duk wani bayani da zai taimaka wajen binciken.

Leave a Reply