Majalisar tsaro ta jihar Kano ta ayyana kwacen waya a matsayin fashi da makami, kuma duk wani mutum ko kungiyar da aka kama da aikata laifin za’a yanke masa hukunci ne a matsayin ‘dan fashi da makami. Kwamishinan yada labarai da harkokin cikin gida mai barin gado Muhammad Garba ne ya bayyana Continue reading
Akalla shugabannin kasashe 20 na duniya ciki har da Afirka ne ke Abuja yanzu haka, domin halartar bikin rantsar da Asiwaju Bola Ahmed Tinubu a matsayin shugaban kasa na 16 a tarihin kasar nan. Bikin rantsar da Tinubu shi ne karo na 7 a jere na mika mulki a dimokuradiyya a cikin shekaru 24 na […]Continue reading
Tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sanya hannu kan kudirin dokar neman a kafa hukumar kula da Almajirai da yaran da ba sa zuwa makaranta domin hana fatara da cin zarafi. Kudirin da Balarabe Shehu Kakale da wasu mutane 18 suka dauki nauyi mai suna: Kudirin dokar kafa hukumar kula da ilimin almajirai ta kasa […]Continue reading
A yau Litinin 29 ga watan Mayu, an rantsar da Zababben shugaban kasa, Bola Tinubu a matsayin zababben shugaban kasa na 7. Ana gudanar da bikin rantsar da sabuwar gwamnatin ne a dandalin Eagle Square da ke Abuja. Gwamnatin Tinubu za ta kasance ta 17 a kasar tun bayan da Birtaniya ta mika wa Najeriya […]Continue reading
An kama wani mutum bayan da aka kashe mutane hudu a wani harin bindiga da wuka da ba a saba gani ba a kasar Japan. Wanda ake zargi da kai harin ya daba wa wata mata wuka tare da harbe wasu ‘yan sanda biyu da bindigar farauta a yankin Nagano. ‘Yan sanda sun bayyana sunan […]Continue reading
An kama daya daga cikin mutane hudu da suka tsere wadanda ake zargi a kisan kare dangi na kasar Rwanda a shekarar 1994. Masu gabatar da kara na Majalisar Dinkin Duniya sun ce an kama Fulgence Kayishema a kasar Afirka ta Kudu kuma ana sa ran zai fuskanci shari’a a Rwanda. An tuhumi tsohon sufeton […]Continue reading
Babban Sakataren Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Gombe, Sa’adu Adamu, a jiya ya ce maniyyata dubu 2 da 556 ne za ayi jigilarsu zuwa Saudiyya daga Gombe ta jirgin saman Air Peace a bana. Sa’adu Adamu ya shaida wa manema labarai a Gombe cewa a ranar 3 ga watan Yuni ne ake sa ran […]Continue reading
Ko’odinetar hukumar matasa masu yi wa kasa hidima ta kasa NYSC reshen jihar Bauchi, Rifkatu Yakubu, ta ce wasu masu yiwa kasa hidima su 5 ‘yan rukunin B kashi na 1 na shekarar 2022, za su maimaita shekarar hidimar su a jihar. Ta bayyana hakan ne a jiya ga Kamfanin Dillancin Labarai na Kasa a […]Continue reading
Gwamna Badaru Abubakar ya kaddamar da hanyar Ringim zuwa Bachawa zuwa Doko wanda aka gina akan sama da Naira miliyan dubu 3 da miliyan 800. Gwamnan ya kuma kaddamar da titunan cikin garin Ringim mai tsawon sama da kilomita hudu da kuma titunan cikin garin Sabongarin ‘Ya’ya kashi na 2. Kaddamar da ayyukan na daga […]Continue reading
Gwamnatin jihar Jigawa ta bada ayyukan tituna sama da 100 a cikin shekaru takwas da suka gabata. Babban sakataren ma’aikatar ayyuka da sufuri Injiniya Datti Ahmed ya bayyana hakan a wajen kaddamar da aikin titin Kwanar Garki zuwa Albasu zuwa Jigawar Dan-Ali wanda gwamnatin mai ci ta sake ginawa. Haka kuma an kaddamar da titunan […]Continue reading