An kama wani matashi bisa laifin bankawa kakarsa wuta

0 146

Rundunar ‘yansanda ta Jihar Jigawa ta kama wani matashi mai dan shekara 26 mai suna Nura Mas’ud, bisa laifin bankawa kakarsa wuta.

Kakakin rundunar ‘yansandan Jiha, DSP Lawan Adam Shiisu ne ya tabbatar da hakan ga manema labarai.

Ya ce sun sami korafi a ƙauyen Ɗan Gwanki da ke ƙaramar Hukumar Sule-Tankarkar , in da wani mai suna Nura Mas’ud ya bankawa kakarsa wuta, yar shakaru 60 a duniya.

Kakakin yan sandan yana mai cewar sun garzaya da ita zuwa asibiti inda likita ya tabbatar da mutuwar ta sanadin kuna. To sai dai, rundunar ‘yansandan ta tabbatar da matashin ba shi da cikakkiyar lafiyar ƙwaƙwalwa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: