Kotun Tarayya da ke Abuja ta yanke wa Halima Haliru Umar hukuncin ɗaurin shekaru 20 a gidan yari bayan ta amsa laifin mallakar harsasai 302 na bindigar AK-47 ba tare da izini ba, tare da yunƙurin tallafa wa ayyukan ta’addanci.
Jami’an DSS ne suka cafke Halima a jihar Filato kafin daga bisani a gurfanar da ita a gaban kotu kan tuhume-tuhume huɗu da suka shafi tsaro.
A yayin zaman kotun, wadda ake tuhuma ta amsa laifuka biyu daga cikin huɗun da ake zarginta da su, lamarin da ya sa Mai Shari’a Hauwa Yilwa ta yanke mata hukunci kai tsaye.
Lauyan Halima, Hamza Dantani, ya roƙi kotun da ta sassauta hukuncin, yana mai bayyana cewa wannan ne karo na farko da ta aikata laifi, kuma tana da jariri ɗan shekara guda da aka kama tare da ita.