IFFHS Ta Saɓa da FIFA, Ta Ayyana Lionel Messi A Matsayin Gwarzon Ɗan Wasan Gasar Kofin Duniya
Hukumar International Federation of Football History & Statistics (IFFHS) ta ayyana kyaftin ɗin Argentina, Lionel Messi, a matsayin Gwarzon Ɗan Wasan Gasar Kofin Duniya ta FIFA ta 2026, bisa bajintar da ya nuna a tsawon gasar.
Hukumar ta sanar da hakan ne a wata sanarwa da ta wallafa a shafinta na intanet, inda ta ce Messi ne ya samu mafi girman maki a tsarin tantance ‘yan wasa da take amfani da shi.
A cewar IFFHS, ana zaɓen gwarzon ɗan wasa ne ta hanyar amfani da bayanan ƙididdiga, waɗanda suka haɗa da:
Makin da ɗan wasa ya samu a kowane wasa,
Yawan ƙwallayen da ya ci,
Yawan kwallayen da ya taimaka aka ci (assists),
Da kuma tasirinsa a wasannin zagayen fitar da gwani (knockout stage).
Hukumar ta ce bayan nazarin rawar da dukkan ‘yan wasan gasar suka taka, Messi ne ya fi kowa samun maki.
Messi ya buga dukkan wasanni bakwai na Argentina a gasar, inda ya kwashe mintuna 626 a fili, ya kuma bayar da gudummawar ƙwallaye 12, bayan ya zura ƙwallaye takwas tare da bayar da taimako huɗu (4 assists).
Haka kuma, ya samu matsakaicin maki 8.33 a kowane wasa, wanda shi ne mafi girma a cikin dukkan ‘yan wasan da IFFHS ta tantance.
IFFHS ta bayyana cewa tsarin tantancewar nata yana bai wa wasannin zagayen fitar da gwani muhimmanci na musamman, saboda irin ƙalubalen da ke tattare da su, tana mai cewa Messi ya ci gaba da taka rawar gani har ya jagoranci Argentina zuwa wasan ƙarshe.
A cikin sanarwar, hukumar ta ce:
“Kwamitinmu ya yanke wannan hukunci ne bisa ƙididdiga da bayanai sahihai, ba saboda suna ko farin jini ba. Lionel Messi ne Gwarzon Ɗan Wasan IFFHS bisa hujjojin da bayanai suka tabbatar.”
Wannan lambar yabo ta ƙara wa Messi jerin manyan nasarorin da ya samu a gasar Kofin Duniya ta 2026, inda ya kasance ɗaya daga cikin fitattun ‘yan wasan da suka fi haskakawa.