’Yan Sanda Sun Kwato Miyagun Kwayoyi 5,916, Sun Kama Dillalai 7 A Jigawa

0 35

’Yan sanda sun kwato miyagun ƙwayoyi 5,916, sun kama dillalai 7 a Jigawa

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Jigawa ta ce ta ƙwace miyagun ƙwayoyi 5,916 da kuma tubalan tabar wiwi guda biyar a wasu samame da ta gudanar a sassan jihar.

Rundunar ta ce samamen, waɗanda aka gudanar bisa bayanan sirri, sun shafi sassan Kazaure, Gumel, Miga, Dutse, Sundumina, Taura, Babura, Ringim, Sara da Aujara.

Daga cikin ƙwayoyin da aka kwato akwai Exol, Tramadol, D5, Diazepam, Taramol, Rubber Solution, Pregabalin da tabar wiwi, yayin da aka kama mutane bakwai da ake zargi da safarar miyagun ƙwayoyi.

Rundunar ta ce an gudanar da binciken farko kan waɗanda ake zargin, sannan aka gurfanar da su a gaban kotuna da suka dace domin fuskantar shari’a. Kwamishinan ’Yan Sandan Jigawa, CP Tijjani Murtala, ya ce rundunar za ta ci gaba da amfani da bayanan sirri da haɗin gwiwar sauran hukumomin tsaro wajen fatattakar masu safarar miyagun ƙwayoyi a jihar.

Leave a Reply